Gwamnati ta ba da hutun bikin Ranar Dimokuraɗiyya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 12 ga Yuni a matsayin ranar hutun gama-gari ga ma’aikata albarkacin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2023.

Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Oluwatoyin Akinlade ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, “Albarkacin wannan rana, ana gayyatar ‘yan Nijeriya da abokan Nijeriya su zo su shaida nasarorin da aka cimma da kuma hanƙoron makoma nagari ga dimokurax’ɗiyyar ƙasar.

Babban Sakataren ya yi amfani da wannan dama waken taya ‘yan Nijeriya murnar bikin Ranar Dimokuraɗiyya na wanna shekar.