Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin Ista

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin Ista na bana, wato Juma’a 15 da kuma Litinin 18 ga Afrilun 2022.

Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Shuaib Belgore ne ya bada sanarwar hutun a madadin Ministar, Rauf Aregbesola.

Rauf ya buƙaci al’ummar kirista a faɗin Nijeriya da su yi amfani da wannnan lokaci na Ista wajen ɗabaƙa halin son juna, zama tare, taimakekeniya, yafiya, kyautatawa da kuma zaman lumana da haƙuri da juna kamar dai yadda Annabi Isa ya karantar a halin rayuwarsa.

Kazlaika, Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar ƙasa baki ɗaya da a ci gaba da yi wa Nijeriya addu’a domin ganin bayan matsalar tsaron da ta addabi sassan ƙasa.

Daga nan, ya bai wa ‘yan ƙasa tabbacin gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen hana aukuwar hare-hare a manyan hanyoyin ƙasa da na jirgin ƙasa da kuma filayen jirgin sama.

Ya ƙarasa da cewa, lamarin tsaro abu ne da ya shafi kowa, don haka ya ce akwai buƙatar ‘yan ƙasa da baƙi kowa ya mara wa ƙoƙarin gwmanati baya wajen samar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.