Gwamnati ta bayyana musabbabin rashin samun wutar lantarki a ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Gwmnatin Tarayya ta bayyana cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki da ‘yan ƙasa ke fuskanta a baya-bayan nan hakan ya faru ne saboda ayyukan wasu ɓatagari.

Cikin sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Asabar, Ma’aikatar Lantarki ta Ƙasa ta ce lalata babban layin lantarki na Odukpani zuwa Ikot Ekpene mai karfin 330kV da wasu ɓatagari suka yi hakan ya sa ƙarfin lantarkin da ake samar wa ƙasa ya ragu da 400MW wanda hakan shi ne dalilin fuskantar matsalar rashin wutar lantarki a faɗin ƙasa a baya-bayan nan.

Mai taimaka wa Ministan Lantarki kan harkokin yaɗa labarai, Isa Sanusi, ya ce ma’aikatar na yin bakin ƙoƙarinta wajen magance wannan matsala.

Babban birnin Tarayya, Abuja da sauran manyan biranen Nijeriya da sauransu sun kasance cikin duhu sakamakon wannan matsalar. Wannan dai ba shi ne karon farko da irin hakan ke aukuwa ba ga fannin lantarkin ƙasar nan a cikin shekara guda.

Su ma kansu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun bada sanarwar matsalar da aka fuskanta, kamar dai yadda aka ga kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KEDC) ya aiwatar cikin sanarwar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Abdulazeez Abdullahi.

KEDC ya sanar da masu amfanin da lantarki a Kaduna cewa matsalar rashin wutar da aka fuskanta hakan ya faru ne sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasa. Tare da cewa, gwamnati na yin bakin ƙoƙarinta domin magance matsalar.

Kamfanin ya bai wa kostomominsa haƙuri kan duk wata matsala da rashin wutar lantarkin ya haifar musu.

Shi ma a nasa ɓangaren, Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC), bai rasa sanar da kostomominsa faruwar wannan matsalar da ta auku a Juma’ar da ta gabata ba. Daga nan ya bai wa yankunan da ke ƙarƙashin kulawarsa haƙuri tare da cewa, hukumar da lamarin ya shafa ta dukufa wajen daƙile matsalar.

Haka dai lamarin yake ga Kamfanin Rarraba Lantarki na Jos da Kamfanin Rarraba Lantarki na Eko da sauran takwarorinsu, baki ɗaya sun tabbatar da faruwar wannan matsala, sun kuma bai duka yankunan da ke ƙarƙashin kulawarsu haƙurin aukuwar hakan.

Ministan Lantarki, Abubakar Aliyu, ya ɗora alhakin aukuwar matsalar a kan rashin kyakkywar kula da cibiyoyin samar da lantarki da kuma ƙarancin man gas.

Daga nan, ya bayyana cewa gwamnati ta ɗaga darajar wasu cibiyoyin samar da lantarki guda huɗu a sassan ƙasa a matsayin wani mataki na bunƙasa fannin lantarki.