Gwamnati ta buƙaci gidajen talabijin su riƙa fassara labarunsu da yaren kurame

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin tashoshin talabijin a faɗin ƙasa su riƙa amfani da yaren kurame a lokutan gabatar da labarai don fassara labarun da suke bayarwa don ƙaruwar masu fama da nakasa.

Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya bada wannan umurni yayin wani taro da suka gudanar ta bidiyo tare da jami’an Cibiyar Kula da Nakasassu, a Litinin da ta gabata a Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaban cibiyar nakasassun, David Anyaele, ya yi ƙorafin an baro masu fama da nakasa a baya game da sha’anin labarun da tashoshin kan bayar balle kuma su san halin da ƙasa ke ciki.

Don haka Anyaele ya ce a madadin masu fama da nakasa su milyan 31 da ake da su a faɗin ƙasa, yana roƙon gwamnati ta saurare su ta biya musu wannan buƙata.

Ministan ya ce za a tura wa gidajen talabijin, mallakar gwamnati da ma masu zaman kansu, umurni a hukumance domin su ɗabaƙa shi.

Ya ƙara da cewa, wannan batu al’amari ne wanda dokar kula da kafafen yaɗa labarai ta hukumar NBC ta san da shi.

Daga nan, Ministan ya bada tabbacin cewa ma’aiktarsa za ta haɗa kai da cibiyar nakasassun wajen tabbatar da cewa dokar da ta hana nuna wariya ga nakasassu na aiki yadda ya kamata.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*