Gwamnati ta ciwo bashin Dala miliyan 800 ne don sauƙaƙa wa talakawa –Ministar Kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An bayyana cewa babban dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 800, shi ne don a sauƙaƙe wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa da su ka tsinci kan su a ciki sanadiyyar annobar Korona, sauƙaƙa matsatsin da su ka fuskanta dalilin ƙarancin kuɗaɗe a lokacin sauya launin kuɗaɗe da kuma tsadar rayuwar da za a afka dalilin cire tallafin fetur da za a yi a cikin watan Yuni.

Hukumar NASSCO ce ta bayyana haka, cikin wata sanarwar da kakakin ta Joe Abuku ya fiyar a ranar Laraba.

Wannan kuɗaɗe dai Ministar Kuɗaɗe, Kasafi da Tsare-tsare Zainab ta ce an ciwo su bashi ne saboda rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da za su afka nan ba da daɗewa ba.

Ta ce aƙalla mutum miliyan 50 ne za su amfana da tsarin.

Makonni biyu da su ka gabata dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin alamomin afkawa cikin tsadar rayuwa a tsakiyar 2023 saboda janye tallafin fetur da za a yi.

A cikin labarin, Gwamnati ta ciwo bashin Dala Miliyan 800, don ta raba wa faƙirai kuɗin tausar-ƙirjin fargabar tsadar rayuwa idan an cire tallafin fetur daga watan Yuni.

Alamomi daga Gwamnatin Tarayya sun nuna tabbas marasa galihu za su ɗanɗana kuɗar tsadar rayuwa daga watan Yuni zuwa ‘illa ma sha-Allahu’, yayin da an kammala shirin janye tallafin fetur, lamarin da zai sa tsadar sa ta sa da yawan masu motocin hawa za a jingine ababen zirga-zirgar na su, saboda tsadar fetur.

Dalilin haka ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fara kinkimo bashin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin ta raba wa marasa galihu ‘yar la’adar tausaya masu dangane da mawuyacin halin rayuwar da za au afka nan gaba daga watan, idan an cire tallafin fetur.

Bashin wanda babu ruwa a ciki, wato a Turance ‘World Bank Facility’, za a raba kuɗaɗen ne ta hanyar tuttura wa marasa galihu miliyan har su miliyan 50, domin a rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su afka nan gaba kaɗan.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa da Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Laraba, a Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron.

Zainab ta ce za a fara raba wa talakawa ta hanyar tuttura masu a asusun bankunan su, amma sai bayan an cire tallafin a watan Yuni tukunna.

Ta ce wannan Dala Miliyan 800 ba ita kaɗai ce za a raba masu ba, akwai sauran wani bashin ya na tafe, wannan somin-tavi ne kawai.

Ta ce tuni akwai rajistar gidajen faƙirai, matalauta da marasa galihu har miliyan 10, waɗanda ta kintata yawan jama’ar da ke cikin lissafin ƙididdigar za su kai mutum miliyan 50. Ta ce waɗannan adadin duk sunayen su na cikin Rajistar Tattara Ƙidayar Marasa Galihu ta Ƙasa.

Zainab ta ce gwamnati a shirye ta ke ta rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwar da za su fuskanta nan gaba, ta wasu hanyoyi ba sai ta hanyar tura masu kuɗaɗen cefane ta asusun ajiyar su na bankuna ba.

“Ƙungiyar Ƙwadago ma akwai yiwuwar ta shigo da tsarin sayen motocin sufuri masu yawan gaske, domin rage wa ma’aikata da marasa galihu tsadar kuɗin mota nan da ɗan wani lokaci idan an janye tallafin fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *