Gwamnati ta jinkirta dawo da aikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da jinkirta dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja da ta ayyana yi a ranar Litinin ɗin nan.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a jiya Lahadi.

Ministan ya mayarwa da ’yan Nijeriya murnarsu ciki a yayin rangadin da ya kai kan layin dogon da ke Kaduna domin tabbatar da matakin shirye-shiryen da aka kammala gabanin dawo da jigilar.

Ministan wanda bai fayyace ainihin ranar da za a dawo da jigilar ba, ya ce jinkirin da za a fuskanta ba zai wuce na tsawon mako guda ba.

A cewar ministan, “Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da wani sabon tsarin siyan tikitin jirgin, wanda a cewarsa shi ne mafarin binciken tabbatar da tsaro wanda zai ba mu damar tantance waɗanda ke hawa jirgin a kowane lokaci.”

A makon da muka yi bankwana da shi ne Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 28 ga watan Nuwamban 2022, a matsayin ranar da za a dawo da aikin jirgin ƙasan da ke zirga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja, babban birnin ƙasar.