Gwamnati ta kashe naira tiriliyan 2 wajen sayen abinci a 2020

Daga UMAR M. GOMBE

Babban Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Sha’anin Tattalin Arziki, Dakta Doyin Salami ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe kusan Naira Tiriliyan 2 wajen sayen kayayyakin abinci daga kasashen ketare tsawon watanni tara, lokacin da dukkanin iyakokin kan tudu ke rufe.

Dakta Salami ya fadi haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan makomar tattalin arzikin kasar nan da ya gudana ta kafar bidiyo a Legas a tsakiyar wannan makon.

A cewar Dakta Salami duk da rufe iyakokin kan tudu da Nijeriya ta yi, sai da gwamnati ta kashe Naira Tiriliyan 1 da biliyan 850 wajen shigo da kayayyakin abinci cikin kasar a tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar shekarar 2020, karin akalla kashi 60 idan aka kwatanta da kudin da aka kashe a 2019.

Ya kuma qara da cewar, makudan kudaden da suka kashe wajen sayen abincin daga kasashen ketare, ya nuna cewar har yanzu kasar nan ba za ta iya ciyar da kanta ba, don haka ya zama dole a sake yi wa tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki garambawul.

Dakta Salami ya ce akalla manoma miliyan 2 da dubu 500 ne suka tafka asarar amfanin gonar da suka noma sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa a shekarar 2019.

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta fitar a watan Mayun shekarar bara, ya nuna cewar a 2019, Naira Tiriliyan 40.21 aka kashe kan kyayyakin abinci da sauran bukatu a Nijeriya, sabanin naira tiriliyan 21.62 a shekarar 2018, abin da ke nuni da karuwar farashin kayayyakin abinci akai akai.