Gwamnati ta sake ɗage shirin ƙidayar al’umma

Gwamnatin Tarayya ta sake ɗage shirin ƙidayar al’umma na 2023.

Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar News Point Nigeria a ranar Asabar cewar, an cimma matakin ɗage shirin ne bayan wata ganawa tsakanin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Nasir Isa Kwarra.

A cewar majiyar, an ɗage shirin ne saboda ƙalubalan da Hukumar NPC ke fuskanta dangane da gudanar da shirin.

Duk da dai majiyar ba ta bayyana matsalolin ba, amma dai a baya hukumar ta dakatar da shirin horar da ma’aikatanta na wucin-gadi saboda rashin kuɗi da sauransu.

Majiyar ta ce ba za ta iya bayyana sabon lokacin da hukumar ta tsayar don gudanar da shirin ba, tana mai cewa Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, zai bayyana hakan ba da jimawa ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumar ke ɗage shirin ƙidayar ba saboda wasu dalilai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *