Gwamnati ta sake tsawaita wa’adin haɗa layin waya da lambar NIN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa’adin haɗa Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da Layin Waya (SIM).

Ministan Sadarwa, Isa Pantami, wanda ya sanar da hakan, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su kammala aikin kafin ƙarshen shekarar 2021.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun masu magana da yawun Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC), Ikechukwu Adinde da Kayode Adegoke.

Dukkan mutanen biyu a cikin wata sanarwa a watan Yuni sun ba da sanarwar 31 ga Oktoba a matsayin ranar ƙarshe na haɗin SIM da NIN. Amma gwamnati ta ƙara wa’adin da ƙarin watanni biyu.

Gwamnati ta yi alƙawarin tabbatar da cewa duk ‘yan ƙasa da masu bin doka da oda da mazauna yankin ba za su rasa damar yin amfani da layukan wayarsu ba matuƙar sun aiwatar da haɗin, inda ta ce za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari a fannin sadarwa.