Gwamnati ta soma nazarin rage albashin ma’aikata don rage kashe kuɗaɗe

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ga dukkan alamu, mai yiwuwa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin zabtare albashin ma’aikatanta a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da take wajen ganin an rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da harkokin gwamnati.

Bayanan Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ne suka nuna haka a Talatar da ta gabata inda ta faɗa cewa lallai, gwamnati na ƙoƙarin duba yiwuwar rage kashe kuɗaɗen da take yi wajen harkokin gudanarwa.

Ta yi wannan bayani ne a wajen taron tattauna batun rashawa da tsadar gudanar da gwamnati a Nijeriya wanda Hukumar Yaƙi da Rashawa da Laifuka Masu Alaƙa da Rashawa Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (ICPC) ta gudanar a Abuja.

Ta ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci Ma’aikatar Lura da Albashi da Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa, ta zauna ta yi nazarin albashin ma’aikatan gwamnati da na saurarn hukumomi domin rage kashe kuɗaɗen da ake yi.

Don haka ta nemi hukumomi su yi aiki daidai da wannan ƙudiri domin rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa duba da yadda samun gwamnatin ke kwan-gaba-kwan-baya.

A cewar Ministar, gwamnati na shirin cire wasu abubuwa daga kasafin da ta yi domin samun sauƙin lamari.

Ta ce, “Har yanzu kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa sai ƙaruwa yake ta yadda ya nunka kuɗaden shigar da muke samu sau biyu. Duk shekara haka ayyukan da ake maimaitawa sukan mamaye kasafin ƙasa waɗanda aiwatar da su bai zama wajibi ba.

“Shugaban ƙasa ya bada umarnin kwamiti mai kula da al’amarin albashi da ke ƙarƙashin jagorancina, ya yi aiki tare da shugaban ma’aikata da sauran mambobin kwamiti wajen nazarin albashin ma’aikata da ake biya domin rage wa gwamnati yawan kashe kuɗaɗe.

A nasa ɓangaren, Shugaban hukumar ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye (SAN), ya lissafo wasu abubuwa da ya ce ya kamata a maida hankali a kansu wajen bincike da suka haɗa da batun ma’aikatan bogi, coge a takardun biyan albashi da kuma maguɗi a sha’anin ɗaukar sabbin ma’aikata.