Gwamnati ta tallafa wa mata 8,000 da kudi N20,000 a Legas

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta kyautata rayuwar talakawa da marasa galihu a fadin kasa inda ta raba wa mata su 8,000 tallafin kudi na naira 20,000 ga kowaccensu a karkashin shirin nan nata na tallafa wa matan karkara da kudade.

Ministar Jinkai da Agaji, Sadiya Umar Farouq ce ta bada jaddadin yayin kaddamar da shirin tallafa wa matan a Legas.

Da take jawabi a wajen taron kaddamar da shirin a bisa wakilcin babban sakataren ma’aikatarta Bashir Nura Alkali, Sadiya ta ce, “Kudirinmu shi ne mu ga mata sama da 8,000 sun amfana da shirin a tsakanin kananan hukumomin jihar Legas baki daya.”

Ministar ta ja hankalin wadanda suka ci gajiyar shirin kan cewa kudin da aka tallafa musu da shi nasu ne, don haka sai su yi amfani da shi wajen bunkasa ‘yan sana’o’insu don kyautata rayuwarsu.

A cewar Sadiya, “An bai wa matan tallafin ne domin inganta rayuwar wadanda lamarin ya shafa, tare da fatan za su sarrafa kudin ta hanyayoyin da suka dace.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Gwamna Jihar Legas Babajide Olushola Sanwo-olu, ta bakin mataimakinsa Dr. Kadiri Obafemi Hamzat, ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya samar da wannan shiri na tallafa wa matan karkara.

Wanda a cewarsa, “hakan ya yi daidai da kudirin gwamnatn jiharmu na neman bunkasa al’umma a karkashin shirin Muradun Bunkasa Al’umma (SDGs).”

Daga nan, Sanwo-olu ya yi kira ga wadanda suka amfana da shirin da su duba su yi abin da aka ba su tallafin domin sa.