
Daga HAMZA RUFA’I
Gwamnatin tarayya ta ce ta yafe harajin da take bin manoma da ƙananan masana’antu biyo bayan gyare-gyaren da aka yi wa tsarin biyan haraji a Nijeriya.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan tsarin kuɗi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele ya faɗi hakan cikin wata sanarwa inda ya ce an ƙaddamar da sabon tsarin biyan haraji wanda zai warware matsalolin kuɗaɗen haraji da ake bi bashi ciki har da ƙananan masana’antu da manoma.
Oyedele, ya ce an fara aiki da tsarin kuɗin harajin da ake bi bashi ne a shekarar 1977 wanda an yi shi ne domin samar da tsarin biyan haraji kafin yin cinikayya na musamman.
Sannan kuma, wani dalilin samar da tsarin shi ne, domin ya taimaka wa gwamnati da hanyoyin karɓar haraji bisa tsari wanda ya dace da kuma kula da shi ta hanyoyin da suka dace.