Gwamnati ta yi wa Magu ƙarin girma duk da zargin rashawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar aikin ‘yan sanda ta tabbatar da ƙarin girma ga tsohon shugaban riƙo na Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya (EFCC), Mustafa Ibrahim Magu zuwa Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, tare da wasu mutane biyar.

AIG Magu Ibrahim wanda ke gargarar yin ritaya, shi ne wanda ya fi kowa girma a tsararrakinsa kuma ya ƙasa samun ƙarin girma har sau biyu bayan da ya dawo hukumar ‘yan sanda daga EFCC.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta tabbatar da ƙarin girma ga John Ogbonnaya Amadi a matsayin mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, domin maye gurbin Marigayi DIG Joseph Egbunike wanda ya wakilci Kudu maso Gabas a tawagar ‘yan sanda.

Haka kuma an ƙara wa Zana Bala Senchi zuwa matsayin DIG.

Sauran waɗanda aka karawa girma zuwa AIG su ne CP Abraham Egong Ayim; Okunlola Kola Kamaldeen; Andrew Amieengheme; Akeera Mohammed Yous; Celestine Amechi Elumelu; Ngozi Vivian Onadeko da Danladi Bitrus Lalas (Airwing).

A wata sanarwa da Ikechukwu Ani, shugaban yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar ya fitar, ya ce an ƙara wa mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 23 girma zuwa kwamishinonin ‘yan sanda.

A wani labarin kuma, Fadar Shugaban Ƙasaasa ita ma ta magantu kan ƙarin girman da aka yi wa Ibrahim Magu da ke shan suka da cece-kuce wajen ‘yan Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, Fadar Shugaban Ƙasaasar ta bayyana ƙarara cewa alhakin yi wa jami’ai ƙarin girma ya rataya ne kan Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda, ba a kan Shugaba Buhari ba.

Garba Shehu ya ci gaba da cewa Buhari ba shi da hannu ko kaɗan a ɗaga darajar jami’an ‘yan sanda a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *