Gwamnati za ta dakatar da ɗaukar nauyin WAEC da sauransu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana cewa ba za a ci gaba da ware wa hukumomi da majalisun ƙwararru kaso daga asusun gwamnati ba ba kamar yadda aka saba.

Gwamnati ta ce wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Janairun 2024.

Darakta Janar na Ofishin Kasafi, Ben Akabueze ne ya bayyana haka a cikin wasiƙar da ya aika wa hukumomi da cibiyoyin da lamarin ya shafa.

Wasiƙar mai ɗauke da lamba DG/BDT/GEN. CORR/2016/XII/3067 da kwanan wata 26 ga Yuni, 2023, ta nuna cewa an ɗauki wannan mataki ne daidai da shawarar Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Albashi (PCS)

Da daman ‘yan ƙasa na ra’ayin cewa wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen rage kuɗaɗen da take kashewa.

Da alama wannan mataki zai shafi har da batun jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da gwamnatin ta saba ɗaukar nauyi.

Majiyarmu ta ce akwai ƙungiyoyi ko majalisun ƙwararru sama da 30 a faɗin Nijeriya wanda wasunsu Gwamnatin Tarayya ce ke ɗaukar nauyinsu.