Gwamnatin ƙasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta ta hanyar ingiza samun wadata ba tare da barin kowa a baya ba

Daga AMINA XU

Abin dake shaida wadata da karfin wata kasa shi ne ƙarfinta na kawar da talauci, kuma shaidar ƙarfin wata gwamnati shi ne matakan da ta ɗauka don rage gibin dake tsakanin mawadata da matalauta.

Tabbatar da samun wadata ba tare da barin kowa a baya ba, daya ne daga cikin wasu muhimman abubuwa dake cikin tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta ƙasar Sin.

Mawadata su taimakawa matalauta wajen fita daga talauci, wata hanya ce mai kyau ta tabbatar da wannan buri.

Ni ne na yi sa’a sosai, saboda iyali na ɗaya ne daga cikin iyalan da suka samu matsaikaciyar wadata a matakin farko, amma a wancan lokaci, wato waje yau shekaru 30 da suka gabata, a lokacin da nake karatu a makarantar firamare, ban san cewa akwai wasu mutane da suke fama da talauci mai tsanani a yankunan karkara ba.

Wata rana, makarantar da nake karatu ta kai mu wani ƙauye, don sanin yadda manoman ƙauye suke da zama, sannan mu ba su wasu kayayyakin jin kai. Wanda na baiwa taimako shi ne wani yaro mai shekaru daidai da nawa, ya kuma gaya min cewa, a baya ya ɗauka cewa, ba zai iya kammala karatun firamare ba sai dai ya nemi wani aikin yi domin taimakawa iyayensu fama da talauci, daga baya gwamnatin wurin ta ba iyalinsa wasu kuɗin tallafi, shi ya sa ya koma makaranta, zaman rayuwar gidansa ma ya samu kyautatu.

A waccan lokaci, ni ƙaramar yarinya ce, ba ni da karfin taimaka masa, amma na san cewa, ina da nauyin dake bisa wuya na a nan gaba, wato dole ne na taimakawa sauran mutane dake fama da talauci idan na samu arziki.

Wani dan jarida ya ga ni da wancan yaro muna rubutawa juna adireshenmu, sai ya tambaye ni dalili, na ba shi amsa cewa, na sa niyyar ci gaba da taimake shi nan gaba.

Na yi imanin cewa, duk ɗaliban da suka halarci wannan aikin da makarantarmu ta tsara, za su fahimci ma’anar samun arziki tare, kuma za su sauke nauyin dake wuyansu na taimakawa waɗanda suke buƙata nan gaba.

Gudanar da irin wannan aiki a cikin makaranta, hanya daya ce daga cikin matakan da gwamnatocin matakai daban daban na ƙasar Sin su kan ɗauka, na ilmantar da yara sanin taimakawa duk wanda yake buƙata.

Masanin ƙasar Birtaniya Martin Jacques ya taba nuna cewa, babban sauyin da Sin take saukewa ya wuce tunanin mutanen yammacin duniya.

Martin Jacques ya fadi gaskiya, tun lokacin kafuwar jamhuriyyar jama’ar ƙasar Sin zuwa lokacin ƙaddamar da manufar yin kwaskwarima a gida da buɗe kofa ga waje, har zuwa sabon zamani na gina zaman al’ummar gurguzu mai sigar halayen ƙasar Sin, gwamantin ƙasar Sin ta kan sanya moriyar fararen hula a gaban kome, ba ta taba mantawa da kowa ba.

Ƙasar Sin ta samu ci gaba da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba, wannan shi ne niyyar JKS ta samarwa dukkan jama’arta zaman rayuwa mai arziki.

A ganin Martin Jacques, Sin tana daidaita matsalar rashin adalci ta hanyar aiwatar da manufar samun arzik tare, abin da manyan ƙasashen yamma har yanzu ba su cimma nasara ba tukuna.

Kawar da rashin daidaito da rage gibin mawadata da matalauta nauyi ne dake wuyan duk wata gwamnati, kuma ya zama dole ga kowace gwamnati.

Amma lokacin da gwamnatin ƙasar Sin ta aiwatar da irin wannan mataki, wasu kafofin yada labarai na ƙasashen yamma sun shafa mata bakin fenti wai cewa, gwamnatin Sin na ƙara ƙarfin mallaka. Idan gwamnatoci biyu da suke kasancewa a gaban jama’a a lokaci daya, wata daga cikinsu ta yi alwashi kawai a maimakon ƙoƙarin cika alkawari, amma wata daban ta kan dauki nagartattun matakai wajen kawar da talauci, da ba da taimako ga waɗanda suke domin ƙoƙarin cika alƙawarinta, ku gaya mana wace kuke so ko kuke buƙata?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *