Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ƙarfafa wa kamfanonin ƙasar gwiwar halartar baje kolin CIIE

Daga CMG HAUSA

Wani jami’in gwamnatin Afirka ta Kudu ya sanar da cewa, kamfanonin ƙasar za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje na ƙasar Sin (CIIE) na shekarar 2022, inda suke sa ran samun fa’ida mai kyau, kuma gwamnati za ta taimaka musu wajen ganin hakan ya tabbata.

Mataimakin babban darakta mai kula da bunƙasa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da samun bunƙasuwa da zuba jari a ma’aikatar cinikayya, da masana’antu da yin takara na ƙasar Lerato Mataboge ne, ya bayar da wannan sanarwa, yayin da yake amsa tambayar wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin wani taron da aka shirya ta yanar gizo kan tasirin baje kolin ga kanana, da matsakaitan masana’antun ƙasar (SMMEs).

Mataboge ya ƙara da cewa, “bikin baje kolin na CIIE, wani muhimmin dandali ne, kuma ba shakka za mu shiga a dama da mu, yana da muhimmanci ga tattalin arzikinmu.

Harkokin kasuwanci wani muhimmin injin ne ga ci gaban tattalin arziki da bunkasuwa.

Akwai yankuna da ƙasashen duniya da dama, da suka yi nasarar fitar da al’ummarsu daga ƙangin talauci zuwa ga rayuwa mai wadata ta hanyar kasuwanci.

Ƙasar Afirka ta Kudu ta halarci bikin CIIE na Shanghai tsawon shekaru hudu a jere. Kuma duk da tasirin annobar COVID-19, kamfanonin ƙasar sun taka rawar gani a bikin baje kolin, inda suka tallata naman sa, da barasa, da shayi, da abalone da sauran kayayyakin amfanin gona masu inganci da ƙasar ke samarwa, inda suka yi fatan samun ribar da ta kai dalar Amurka miliyan 210 a shekarar 2020.

Haka kuma sun yi fatan samun riba a sayar da barasa, da abalone, da ‘ya’yan itatuwa, da shayi, da karo, da sauran kayayyaki na kusan dalar Amurka miliyan 38 a shekarar 2021, wanda hakan ya aza wani kyakkyawan ginshiki ga kayayyakin Afirka ta Kudu masu inganci, don fadada kasuwarsu a ƙasar Sin.

Za dai a gudanar da bikin CIIE karo na biyar a birnin Shanghai daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban wannan shekara.

Fassarawar Ibrahim Yaya