Gwamnatin Amurka ta yi rashin dattaku na ƙwace kuɗaɗen ceton rayuka a Afganistan

Daga CRI HAUSA

A ranar 11 ga wata, shugaban ƙasar Amurka Joe biden, ya sa hannu kan wani umurni game da kuɗin babban bankin ƙasar Afganistan dake Amurka da aka hana amfani da su, inda aka bayyana cewa, Amurka za ta raba kuɗin da yawansa ya kai dala kusan biliyan 7 kasu biyu, wato za a yi amfani da rabinsa domin biyan kuɗin diyya ga waɗanda suka rasa rayuka ko suka ji rauni yayin haɗarin jirgin saman da ya faru a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, saura rabi kuma, gwamnatin Amurka za ta yi amfani da kuɗin domin samar da tallafi ga al’ummun Afganistan, amma ba za ta tattauna batun da gwamnatin Taliban ba.

Da zarar al’ummun ƙasa da ƙasa suka ji labarin, sai sun kaɗu matuƙa, saboda sun ga gwamnatin Amurka ta ƙwace kuɗin ceton rayukan al’ummun Afganistan a fili!

A tsakiyar watan Agustan bara, bayan da dakarun Taliban suka mamaye birnin Kabul, fadar mulkin ƙasar Afganistan, daga lokacin gwamnatin Amurka ta hana a yi amfani da kuɗin babban bankin ƙasar dake ƙetare, ciki har da dala biliyan 7 da aka adana a ƙasar ta Amurka, haƙiƙa kuɗin babban bankin Afganistan, kuɗi ne na al’ummun ƙasar, bai dace Amurka ta yi amfani da su ba, lamarin dai, ya bayyanawa duniya ƙarara rashin dattakun gwamnatin Amurka.