Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani likitan ɗan Nijeriya da ke ƙasar Birtaniya ya rasa damar sa hannun gwamnati na cigana da riƙe ɗansa mai shekaru 16 bayan ya yi masa bulala.
Wata mai fafutukar kare haƙƙin yara da aka fi sani da Pepstalk1 ta bayyana hakan a shafinta na Instagram ranar Laraba.
Ta bayyana cewa, likitan ɗan Nijeriya ya yi wa ɗan nasa bulala bayan ya kama shi da abokansa suna kallon wani faifan bidiyo da bai dace ba.
An ruwaito abokansa sun sanar da ’yan sanda kuma suka gaya musu cewa a lokacin da uban yake dukan ɗansa da bel, likitan ya maimaita cewa, “Shin haka ka ke son zama likita?”
Ta ce, “Abokan ɗan wani likitan Nijeriya ne wata biyu da suka wuce suka zo gidan likitan domin su kwana su yi karatu a shirye-shiryen jarrabawarsu ta gama sakandare.
“Da ƙarfe uku na dare, likitan ya shiga ɗakin yaron kuma ya kama su suna kallon wani faifan bidiyo da bai dace ba, mahaifin ya fusata da ɗansa kuma ya doke shi da bel a gaban abokansa.
“Abokan biyun sun fito da gudu domin kiran ‘yan sanda, inda daga baya suka zo suka tafi da yaron. Daga baya an gabatar da shari’ar a gaban kotu kuma yayin zaman, abokanan sun ce sun ji mahaifin na cewa “haka ka ke son zama likita?”, yana dukan ɗansa.
“Yaron ya kuma ce kullum mahaifinsa yana dukansa don ya karanci abin da ba ya so kuma mahaifinsa yana son ya karanta aikin likita a jami’a.