Gwamnatin Jigawa ta kashe Naira miliyan 40,000 wajen biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta biya haƙƙoƙin ma’aikatan jihar kusan miliyan dubu 40 daga watan Mayu na 2015 zuwa Maris na shekarar 2022.

Sakataren zartarwar hukumar asusun adashen gata na jihar, Alhaji Kamilu Aliyu Musa, ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewar, adadin kuɗin ya tasamma fiye da Naira miliyan dubu talatin da tara da miliyan ɗari tara da goma sha takwas a matsayin haƙƙoƙin ma’aikatan.

Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya ce haƙƙoƙin ma’aikatan da asusun ya biya a waɗannan shekaru sun haɗar da giratuti ga ma’aikatan jiha da ƙananan hukumomi da kuma na sashen ilmi.

Sai kuma haƙƙoƙin magadan ma’aikatan da suka rasu a bakin aiki da cikon kuɗin fansho ga masu karɓar fansho da suka rasu alhali ba su cika shekaru 5 suna karɓar fansho ba.
Kazalika, an kuma biya haƙƙoƙin ma’aikatan da aka mayar wa kuɗaɗen asusun adashen gata na kaso 8.

Sakataten zartarwan ya ce asusun ya biya kuɗaɗen fansho na wata har Naira miliyan dubu 25 da miliyan 661 ga ‘yan fansho na jiha da ƙananan hukumomi da kuma na sashen ilmi.

Yana mai nuni da cewar, a zancen da ake yi yanzu aikin tantance ‘yan fanshon da ake kan gudanarwa, yana tafiya bisa tsari kuma yadda ya dace.

Kamilu Aliyu Musa, ya yaba wa jami’an hukumar da shugabannin ƙananan hukumomi da na ƙungiyar ‘yan fanshon jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke ba su a yayin gudanar da aikin tantancewar.