Gwamnatin Jigawa ta raba babura ga ƙungiyar mahauta a ƙananan hukumomin jihar

Daga UMAR AIƘILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa, ta raba babura 27 ga shugabannin ƙungiyar mahauta na ƙananan hukumomin jihar nan 27.

A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a mayankar dabbobi ta Dutse, gwamnan jiha, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce hakan na daga cikin ƙudirin gwamnatin jiha na tallafa wa ’yan qungiyar domin su ji daɗin gudanar da ayyukan su.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ƙananan hukumomi, Alhaji Kabiru Hassan Sugungun, ya ce gwamnati ta sahalewa shugabannin ƙananan hukumomi, su duba buƙatun ’yan ƙungiyar da suka haɗa da gyaran mayankar dabbobi na ƙananan hukumomi, tare da gina musu wasu sabbi da kuma gabatar da rahotan ga gwamnati.

Ya kuma ba su tabbacin samar musu da hanyoyin dogaro da kai domin inganta rayuwarsu.

A jawabinsa na godiya, shugaban ƙungiyar mahauta na jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Mai-Doki ya bayar da tabbacin haɗin kai da goyan bayan ’yan ƙungiyar na cigaba da marawa manufofi da tsare-tsaren gwamnati baya.

Ya kuma buƙaci goyan bayansu kamar yadda suka ba su a baya lokacin zaɓen da ya wuce saboda haka ne ma ya sa ya ke miƙa ƙoƙon bararsu a wajen mahautan.

Da ya ke nasa jawabin, Alhaji Mai fulani Dutse ya buwaci gwamna badaru ya ƙara samar da gine-gine irin na zamani a fikin mayankar ta su da ke Dutse, ya kuma buƙaci asaka ’ya’yansu cikin waɗanda gwamnati za ta tallafawa da jari.

Ya kuma buƙaci gwamnati da ta ba su alawus musamman sarakunan fawa da ke jihar a ɗaukacin ƙananan Hukumomin jihar 27.

Shima shugaban ƙungiyar Alhaji Muhammad maidoki ya gode wa gwamna Badaru Abubakar akan irin gudunmawar da ya ke bai wa jama’ar jihar jigawa ta fuskar inganta rayuwar al’umma.

Ya ƙara da cewa, ko wuta aka hura idan Badaru ya shiga za su bi shi a siyasa, duk inda gwamna Badaru ya ce su yi za su yi, domin dukan ’ya’yan mahauta a jihar magoya bayan APC ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *