Gwamnatin Jihar Katsina ta ba ƙaramar hukumar Kurfi tallafin takin zamani 17,000

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙaramar hukumar Kurfi Garba Abdullahi Kanya ya faɗi haka a lokacin da yake hira da manema labarai a ofishin sa.

Ya bayyana cewa rumfar zaɓe guda 272, inda kowace rumfa ta sami buhu hamsin na takin zamani.

“Haka kuma ƙaramar hukumar ta zaɓi manyan manoma guda goma daga kowace rumfar zaɓe, suma kowannan ya samu buhu goma”.inji Abdullahi kanya.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce wannan tallafi na gwamnan yasa kasuwar taki a yankin ya tsaya cik.

“Haka kuma tallafin ya sa farashin kayan abinci yayi ƙasa”Abdullahi Kanya ya ce .

Ƙaramar hukumar ta gudanar da wasu aikace-aikace na raya ƙasa da suka haɗa da gina hanya daga Ƙafur zuwa Mahuta.

Ya kuma samar da manyan yankuna biyar domin samar da wadataccan ruwan sha da gina masallacin juma’a a mayan garuruwa guda biyar a ƙaramar hukumar.

Kan kiwon lafiya, ƙaramar hukumar ta gina asibitoci guda uku da ɗaukan malaman kiwon lafiya guda 80.