Gwamnatin Kaduna ta ƙaddamar da rajistar masu aikata fyaɗe ta fasahar zamani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaddamar da rijistar masu aikata laifuka ta fasahar zamani ‘dijital’ a ƙoƙarinta na daƙile matsalar fyaɗe a jihar.

Mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe, ta ƙaddamar da rijistar dijital ɗin a ma’aikatar shari’a ta jihar, a wani taron da ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

A nata jawabin, Dakta Balarabe ta ce, a cikin watan Satumba na 2020, Gwamna Nasir El-Rufai ya sanya hannu kan dokar hukunta masu fyaɗe da kuma yi wa waɗanda aka samu da laifin yi wa yara ’yan ƙasa da shekara 14 dandaƙa mai tsauri.

Ta ce, jihar na qara ɗaukar matakai ta hanyar ƙaddamar da rajistar masu laifin aikata fyaɗe, da rubuta sunayensu da kuma kunyata masu laifin domin hana wasu shiga harkar.

Mataimakin gwamnan ta ƙara da cewa, za a haɗa da bayanan masu aikata fyaɗe tare da ‘National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons’ (NAPTIP) ta ƙasa.

Gwamnatin ta lura da cewa, ƙaddamar da shirin ya sanya Kaduna ta zama jiha ta 12 a cikin Tarayyar Nijeirya da ke da rijistar masu aikata fyaɗe.

Rijistar gabaɗaya ta haɗa da sunan mai laifin, adireshin, kamannin jiki, da tarihin aikata laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *