Gwamnatin Kaduna ta tsawaita wa’adin tashi da ta bai wa dillalan motoci

Daga WAKILINMU

Hukumar Tsarawa da Bunƙasa Birane ta Jihar Kaduna ta amince da roƙon Ƙungiyar Masu Sayar da Motoci ta Jihar Kaduna inda ta buƙaci a ƙara wa mambobinta lokaci game da tashi daga inda suke da aka buƙace su da yi.

A wata takardar sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 21, Afrilu, 2021 wadda Stephen Baji ya sanya wa hannu a madadin Darakta Janar na hukumar, ta nuna an ƙara wa waɗanda lamarin ya shafa wa’adi zuwa mako guda bayan watan Ramadan, wato 19 ga Mayu, 2021.

Da wannan, hukumar ta ce ana buƙatar mambobin ƙungiyar su bi umarni su kwashe kayansu ya zuwa wa’adin da aka tsayar na su tashi daga inda suke a yanzu su gwamanati wuri.

Tun a ranar 19 ga Afrilu, 2021 masu sayar da motocin suka aika wa hukumar wasiƙar neman alfarmar a ƙara musu wa’adin umarnin tashin da aka ba su.