Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon gidan sauro miliyan takwas kyauta

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Yaƙi da cutar Zazzavin Cizon Sauro ta Duniya sun ƙaddamar da rabon gidan sauro guda miliyan 8.8 mai ɗauke da sinadarin maganin ƙwari ga magidanta a Jihar Kano, kamar yadda Daraktan Yaɗa Labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa Fagge ya Shaida wa manema labarai a Kano.

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a lokacin qaddamar da yaƙi da zazzavin cizon sauro zuwa gida-gida kyauta a faɗin ƙananan hukumomin Jihar Kano 44 daga ranar 10  zuwa 22 ga watan Nuwambar 2022.

Gwamnan wanda mataimakinsa kuma ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ranar Larabar nan, wanda aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Gaya, inda aka ƙaddamar da rabon domin yaƙi da cutar cizon sauro tare da rigakafin cutar a Jihar Kano.

A cewarsa, ƙaddamar da rabon za a yi amfani da jami’an gudanar da shirin  sama da mutum dubu ashirin, an kuma raba gidan sauro zuwa wurare sama da dubu uku da ɗari shida a faɗin mazavu 484 na Jihar Kano.

Ya bayyana cewa, rabon gidan sauro wani ƙoƙari ne na Gwamnatin Kano domin inganta lafiya da kyakkyawar makomar jama’ar Kano, ya ƙara da cewa, Gwamnatin Kano ta amince da samar da magungunan sauro na wata-wata tare da rabon magungunan domin magance zazzaɓin cizon sauro tsakanin mata masu juna biyu da ƙananan yara.

Kan haɗin gwiwar yaqi da zazzavin cizon sauron, Gwamna ya bayyana cewa ana sa ran sama da mutum miliyan goma sha huɗu masu shekaru tara  zuwa arba”in da huɗu domin samun kyakkyawan sakamako na samun kariya daga cutuka ta hanyar kyakkyawan tsarin rigakafi na yau da kullum wanda ya haɗa da allurar Korona da rijistar haihuwa.

“Don haka ya buƙaci jama’a da ke tsakanin waɗannan shekaru masu tasiri da su yi amfani da kyakkyawar dama domin gabatar da kawunansu ga cibiyon rigakafin domin samun allurar wanda zai taimaka wajen ingantacciyar garkuwa ga zazzaɓin cizon sauro.”

Da yake nuna godiyarsa bisa ci gaba da goyon baya da cigaban haɗin guiwa tare da sarakunan gargajiya domin kakkabe zazzaɓin cizon sauron, Gwamnan ya kuma buƙaci magidanta da su bada haɗin kai ga jami’an da aka tura domin gudanar da aikin domin samun nasarar shirin.

Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehanire wanda Darakta a Ma’aikatar Mr. Festus Okoh ya wakilta ya bayyana cewa Jihar Kano ta kasance guda cikin jihohi bakwai da za su amfana da wannan gagarumin rabon gidan sauron na wannan shekara.

Ya ci gaba da cewa, cikin ƙoƙarin gwamnatoci da abokan haɗa guiwa sun samu gagarumar nasara a yaƙin da ake da cutar Zazzaɓin Cizon Sauro a ƙasar nan ta hanyar amfani da gidan sauro ga yara ‘yan lasa da shekara biyar daga kaso 49.4 a shekara ta 2015 zuwa kaso 58.0  a shekara ta 2018, wannan da sauransu su taimaka wajen rage yaɗuwar Cutar Zazzaɓin Cizon Sauro daga kaso 42.0 a shekara ta 2010 zuwa kaso 27.0 a shekara ta 2015 zuwa kaso 23.0 a shekara ta 2018.

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim, Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano Alhaji Bala Usman Muhammad kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa, wakilan haɗin guiwar na duniya da sauran masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *