Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars (Sai Masu Gida).
A cewar sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce, gwamnati ta naɗa shugaban hukumar da mambobi da sakatare da suka haɗa da:
- Babangida Little, Shugaba
- Garba Umar, Member
- Naziru Aminu Abubakar, memba
- Bashir Chilla, memba
- Ali Nayara Mai Samba, memba
- Shuaibu Ibrahim Doguwa, memba
- Rabiu Pele, memba
- Muhammed Danjuma, memba
- Sabo Chokalinka, memba
- Abba Haruna (Dala FM), mamba
- Engr. Usman Kofar Na’isa
- Yakubu Pele, mamba
- Comrade Sani Ibrahim Coach, Sakatare.
Sanarwar ta ƙara da cewar, a ranar Talata aka ƙaddamar da hukumar.