Gwamnatin Kano ta biya Ja’afar Ja’afar diyyar ɓata sunansa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta baiwa shahararren Dan jaridar nan Ja’afar Ja’afar Naira 800,000 saboda ɓata masa suna da ta yi,

Jiya Juma’a ne dai Ja’afar Ja’afar ya sanarwa Freedom Radio Kano cewa, an biya shi kudin, kamar yadda kotu ta bada umarni da a biya shi Naira dubu 800,

Tun a watan Yulin wannan shekarar ne dai babbar kotun Kano mai lambar 9 da ke zaman ta a Bampai ƙarƙashin mai Shari’a Baba na Malam ta umarci gwamnatin Kano ta biya Ja’afar Ja’afar da kamfaninsa ƙudin, saboda ɓata masu lokaci da aka yi a wajen shari’ar,

In dai ba’a manta ba an dai shafe Shekarau hudu kenan ana fafata shari’a tsakanin Ja’afar Ja’afar da Gwamnan Kano, bayan fitar da masu fayafayan Bidiyo na yadda gwamnan ya ke sunƙuma dalolin Amurka a Aljihun sa na babbar riga.