Gwamnatin Kano ta haɗa hannu da bankin Musulunci don gina makarantun Turanci da Larabci

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin, Abba Kabir Yusuf, ta sanar da shirinta na haɗin-gwiwa da Bankin Musulunci (IDB) don samar da makarantu guda huɗu da za riƙa amfani da yarukan Turanci da Larabci wajen karantar da ɗalibai.

A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya ce gwamantin ta yanke hakan ne a ƙoƙarinta na bai wa yara almajirai damar koyon karatun zamani tare da rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da raba kayan makaranta 789,000 ga ɗalibai daga makarantun gwamnati guda 7,092 na ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar.

Da ya ke jawabi a taron wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Abba ya jaddada batun inganta harkar ilimi a matsayin babban abin da gwamnatinsa ta saka a gaba.

Ya ce, “an yi garambawul ga tsarin tsangayunmu don tabbatar da kammala makarantu a dukkanin kananan hukumomi.”

Gwamnan ya kuma bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu waɗanda a cikin akwai batun dokar ta-ɓaci a harkar ilimi wanda ya sa aka gina sabbin ajujuwa guda 336 da gyaran 119 da suka lalace da kuma samar da kujerun ɗaukar karatu na zaman mutum uku da wasu guda 53,000.

Bugu da ƙari, sama da littafan rubutu miliyan 1.3 ne aka raba wa ɗalibai da kuma ƴan mata 45,000 da suka amfana da tallafin N20,000 ga kowannen su daga tsarin ‘conditional cash transfer’ don tallafa wa karatukansu.

Har’ilayau, Gwamna Abba ya yi godiya ga al’ummar jihar bisa goyon bayansu tare da alƙawarin cigaba da samar musu da ayyukan ci-gaba.

Ana tsammanin haɗe kai da bankin IDB da gwamnatin ta yi, zai taimaka wa bunƙasa harkokin ilimi a jihar da kuma magance matsalolin yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a arewa.