Gwamnatin Kano ta naɗa sabbin shugabannin ma’ikatu da hukumomin lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin shugabannin wasu ma’aikatu da hukumomin lafiya don tafiyar da su yadda ya kamata.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai da yammacin Laraba,
Sanarwar ta ce naɗin na su ya fara aiki ne nan take.

Waɗanda aka naɗa ɗin sune kamar haka: Dr. Mansur Mudi Nagoda, Executive Secretary, Hospital Management Board (HMB); Dr. Nasir Mahmoud, Executive Secretary, Kano State Primary Healthcare Management Board (SPHMB); Farfesa Salisu Ibrahim Ahmed, Executive Secretary, Private Health Institutions Management Agency (PHIMA).

Sauran sun haɗa da: Dr. Fatima Usman Zahraddeen, Executive Secretary, Kano State Health Trust Fund (KHETFUND); Pharm. Ghali Sule, Director General, Drugs and Medical Consumables Management Agency (DCMA); Dr. Usman Bashir, Director General, Kano State Agency for the Control of AIDS (KSACA); Dr. Aminu Magashi Garba, Coordinator, Kano State Cancer Care Centre (KCCC); sai Dr. Muhammad Abbas, Coordinator Kano State Agency for Disease Control (KADC).