DAGA MUKHTAR YAKUBU
Masu iya magana dai sun ce “Ganimar yaƙi ta mayaƙi ce” Da alama wannan karin magana ya zo daidai ga wasu daga cikin jaruman fim da suka bayar da tasu gudunmawar a wajen yaƙin neman zaɓen Gwamnatin Kano ta Abba Kabir Yusif, inda a ‘yan kwanakinnan aka raba musu wasu dalla-dallan motoci tare da kuɗin yin lamba da kuma shan mai.
Wannan rabon motocin da Gwamnatin Kano ta yi a ƙarƙashin ofishin babban mai taimakawa gwamna a kan harkokin wallafe-wallafe, ‘yan fim da dama da suka taka rawa a tafiyar Kwamkwasiyya sun samu. Ko da yake babban mai taimaka wa gwamna a kan harkokin wallafe-wallafe Tajjani Gandu ya nuna cewar tsarin yanzu aka fara, za a ci gaba da fito da waɗanda suka bayar da gudunmawa a tafiyar domin kyautata musu domin su san ana sane da irin gudunmawar da suka bayar a tafiyar.
Cikin waɗanda aka bai wa motocin dai sun haɗa da Alhssan Kwalle, Aina’u Ade, Bashir Nayaye, Dan magori, Yahanasu Sani, Baba Sogiji Isiyaku Jalingi, Hassana Musa da Hussaina Musa.