Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta rage wa ɗalibai ‘yan asalin jihar da ke karatu a makarantun gaba da sakandare kuɗin makaranta da kaso 50%.
Kwamishinan Ilimi mai zurfi na jihar, Dr. Yusuf Ƙofar Mata ne ya sanar da haka a ranar Litinin, yayin da ya ke ganawa da manema labarai.
Ƙofar Mata ya ce, gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin ta rage wa iyaye raɗaɗin biyan kuɗin makaranta sakamakon matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta, sakamakon cire tallafin man fetur.
Ya kuma ce ragen kuɗin makarantar ya shafi ɗaukacin ɗalibai da ke karatu a manyan makarantu mallakar gwamnatin jihar Kano a zangon karatu na 2023/2024.
Makarantun su ne Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aiko Ɗangote Wudil (ADUST), Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) da Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi.
Ragowar sun haɗa da, Kwalejin fasaha ta jihar Kano (Polytechnic), da Kwalejin nazarin ilimin shari’a (Legal), Kwalejin harkokin Noma ta Audu Bako Dambatta, Kwalejin share fagen shiga jami’a ta Rabi’u Musa Kwankwaso da ke Tudun Wada da kuma Kwalejin Ilimi ta jihar Kano.
Dakta Yusuf ya ce, ɗaukar wannan mataki na da alaƙa da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na haɓaka harkokin ilimi.
Sannan ya tabbatar da aniyar gwamnatin na bunƙasa harkokin ilmi, inda ya ce, ganin yadda gwamnatin Kano ta dawo da shirin kai ɗalibai ƙasashe waje nan bada daɗewa ba za a ƙaddamar da tashin ɗalibai kimanin 1,000 da za su fita ƙetare don karo karatu.