Gwamnatin Kano ta sha alwashin tabbatar da adalci ga Hanifa

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Gwamnan jihar Kano ta ƙarƙashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayar da tabbacin cewa za ta ci gaba da sanya ido sosai tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin badaƙalar yin garkuwa da kisan gilla da aka yi wa Hanifa Abubakar, ɗaliba ‘yar shekara biyar a Kwanar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nassarawa, jihar Kano.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa Labaran Jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar.

Gwamnan ya ce tuni matakan da aka ɗauka a lamarin sun haɗa da rufewa da kuma janye lasisin gudanar da makarantar ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya ce gwamnati ta damu matuƙa yadda mutanen da aka damƙa wa kulawar yara suka zama masu kashe su.

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa, gwamnati na tuntuɓar iyalan yarinyar kuma za ta ci gaba da kasancewa da su har sai an tabbatar da adalci a shari’ar don ya zama izina ga wasu.

Gwamnan wanda ya yaba wa jami’an tsaro a jihar kan ɗaukar matakin da suka kai ga cafke waɗanda ake zargi da hannu a cikin lamarin, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da bincike gwamnati za ta bibiyi lamarin da kyau har ma ta kai ga gaci.

Ya kuma yaba wa ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin dan’Adam da kuma ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da suka damu da lamarin.

Haka nan Ganduje ya ba da tabbacin goyon bayan hukumomin tsaro na gwamnati wajen gudanar da ayyukansu na ganin cewa Kano ta samu zaman lafiya.