Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Mai bai wa Gwamnan Kano shawara na musamman kan namun daji da gandu daji, Hon. Ahmad Halliru Sawaba ya ce gwamnatin jihar Kano za ta yi ƙoƙari wajen ganin ta dawo da tallafin da wata cibiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta so ta kawo wa al’ummar Jihar Kano don tallafa masu a harkar kiwon kaji amma gwamnatin da ta gabata ta daƙile.
Ya bayyana haka ne a yayin wani taro da mai bai wa gwamna shawara kan jam’iyyun gama kai Jamilu Abba ya yi da ƙungiyoyi a safiyar ranar Talata.
Ya ce irin wannan tallafi ba sabon abu ba ne, jihohi da dama sun amfana, amma da aka samu irin wannan dama ta zo wa jihar Kano sakamakon wani ɗan asalin jihar Kano da yake shugabantar hukumar da ke da cibiya a jihar Oyo suka nemi a kawo tsarin za su biya kuɗin da yanda za a gudanar tsarin a Kano amma gwamnatin baya ya zo da son rai.
Ya ce a tsarin, kowace ƙaramar hukuma an tanadar mata Naira biliyan ɗaya duk ƙungiya za a ba su N10,000,000 mutane 100 a kowace ƙaramar hukuma.
Ya yi nuni da cewa kowace ƙaramar hukuma za ta samu Naira biliyan ɗaya kenan, amma kasancewar wasu abubuwa da gwamnatin baya ta zo da shi na son rai sai abin bai yiwu ba.
Ya ce amma kusan an gama tsare-tsaren komai kasancewar da wannan gwamnatin ta Injiniya Abba Kabir Yusuf aka ce a je a samu gwamna a yi wannan magana.
Hon. Ahmad Halliru Sawaba ya shaida wa ‘yan jarida cewa kuɗaɗen sun kai Naira biliyan 44 kowace ƙaramar hukuma biliyan ɗaya kuma za a ɗauki mutum 100 a kowace ƙaramar hukuma shine ya kama N10,000,000 kowace ƙungiya za a bayar.
Ya ce son zuciya na waɗanda suke da madafun iko a baya ne ya kawo tarnaƙi, amma yanzu lokaci ya yi Gwamnatin Injiniya Abba Kabir da yardar Allah za ta shiga gaba a aiwatar da tsarin don tabbatar da al’ummar jihar Kano sun ci gajiyar shirin.
Hon. Ahmad Halliru Sawaba mai bai wa Gwaman Kano Abba Kabir Yusuf shawara na musamman kan namun daji da gandun daji ya ce wannan magana ta taso ne shekaru biyu da suka gabata a Gwamnatin Ganduje, don haka yana kira ga mutanen Kano su kwantar da hankalinsu wannan gwamnati mai ci ta talakawa ce, kuma za ta yi iya ƙoƙarinta ta ga ta shiga ta fita ta samo duk wani abu da zai tallafawa cigaban al’umma.
Tun da farko mai baiwa gwamna shawara na musamman kan jam’yyun gama kai, Hon. Jamilu Abbas wanda kuma shine shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Kanon, ya ce sun zo taron don ganawa da ƙungiyoyin jam’yyun gama kai na ƙananan hukumomin ƙwaryar birni don shaida musu manufofin da gwamnati ke so ta bijiro da su don tallafa musu da cigaban al’umma.
Ya ce zai yi aiki da shawarwari da aka bayar domin haɗuwa a ciyar da Kano gaba, ya yaba da yadda ‘yan jam’iyyun gama kai suka nuna masa su masu zuciya ne,masu zaman kansu da aƙida da riƙe alƙawari da jajircewa kuma da yardar Allah bada jimawa ba za a ga wani abu na cigaba.
Hon. Jamilu Abbas ya ce kasancewar an bar ƙungiyoyin jam’yyun gama kai a baya ba tare da shiga lamarinsu ba a wannan Gwamnati ta Injiniya Abba Kabir Yusuf za su farfaɗo da su a dukkanin mazavun jihar Kano gaba ɗaya dan kyautata cigaban al’umma a kowanne ɓangare.
Taron ya samu halartar ɗinbin ‘yan ƙungiyoyin jam’yyun gama kai maza da mata ya kuma sami halartar wasu daga masu muƙaman siyasa da suka haɗa da mataimaki na musamman ga Gwamanan Kano Hon. Ɗan Sani Hotoro.