Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin ƙarshe na aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar ta hanyar ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa mai ƙarfi.
Mataimakin gwamnan jihar, Faruk Lawal joɓe wanda ya wakilci Gwamna Dikko Raɗɗa, ya ƙaddamar da kwamitin ne a Gidan Gwamnatin jihar, a ranar Juma’a.
Kwamitin, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari ke shugabanta, an ba shi wa’adin makonni uku don ya miƙa cikakken rahotonsa kan tsarin aiwatar da sabon albashin.
Aikin kwamitin ya haɗa da dukkan rukunan mai’aikatan gwamnatin jihar, ƙananan hukumomi, da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi.
“Wannan gwamnati ta san irin ƙalubalen tattalin arziƙi da ma’aikatanmu ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur”, inji mataimakin gwamnan.
Ya ƙara da cewa,
ƙirƙirar kwamitin ya nuna jajircewar gwamnatin Dikko Raɗɗa wajen magance waɗannan ƙalubale ta hanyar tsari na aiwatar da mafi ƙarancin albashi mai kyau da ke ɗauke da gyare-gyaren da suka dace.
Kwamitin ya ƙunshi Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari a matsayin shugaba, sai shugaban ma’aikatan jihar, Falala Bawale da babban ma’ajin jihar, da kwamishinonin kuɗi da na kasafin kuɗi da na kananan hukumomi da masarautu da suaran su.
Ƙungiyoyin ƙwadago na da wakilci daga shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya da ta kasuwanci (NLC da TUC), yayin da ɓangaren ƙananan hukumomi su ma aka samu wakilci.
A jawabinsa, Shugaban kwamitin, Abdullahi Garba Faskari ya yi alƙawarin samar da tsarin aiki mai ɗorewa cikin wa’adin da aka ƙayyade wa kwamitin.
“Kwamitinmu zai yi aiki tuƙuru don samar da cikakken tsarin aiwatarwa wanda zai amfani ma’aikata da jihar baki ɗaya”, inji Faskari.