Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙarshe dai gwamnatin jihar Katsina ta amince ta biya mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.
Hakan ya biyo bayan ɗaukar tsawon lokaci ana tattaunawa tsakanin jami’an gwamnatin jihar da ƙungiyar ƙwadago kafin a cimma matsaya.
Sakataren gwamnatin jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari ya jagoranci gwamnatin jihar inda ya ce gwamnatin jihar zata fara biyan sabon tsarin albashin daga watan ƙarshe na wannan shekara.
Barista Faskari ya ƙara da cewa sabon tsarin albashin ba zai shafi tafiyar da ayyukan gwamnati na bunƙasa jihar ba.
Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na kyautata ayyuka da jin-daɗin ma’aikata a jihar.
Kungiyar ƙwadago na ƙasa reshen jihar, ta nuna gamsuwa da matakin gwamnati na amincewa da biyan sabon tsarin albashin wanda zai rage wa ma’aikata halin ƙunci da ake ciki.
Sannan, akan haka ne ake sa ran ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), ta janye jihar Katsina a cikin jihohin da ta umurta da su fara yajin aiki.