Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta bada tallafi na Naira miliyan 36 ga iyalan mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Batsari da Dutsinma na jihar.
Mataimaki na musamman kan yaƙi da ta’addanci da kula da ƴan gudun hijira, Alhaji Sa’idu Ibrahim Ɗanja ya miƙa kuɗin ga iyalan mutanen a madadin gwamna Dikko Raɗɗa.
Alhaji Sa’idu Ɗanja ya jajenta wa iyalan mutanen da ƴan bindiga suka kai wa addaba a yankunan tare da jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na kawo karshen ta’addanci a jihar.
Ƙauyukan da abin ya shafa sune; Gidan Kyari, Tsawa Tsawa, Tudun Dole, Ƴan Shantuna, Kuki da Zangandu a ƙaramar hukumar Dutsinma.
Sai ƙauyukan Goje, Sawanawa, Sahalawa da kukar Toro dake ƙaramar hukumar Batsari.
Shugaban ƙaramar hukumar Batsari, Hon. Mamman Ifo ya yaba wa gwamnatin Dikko Raɗɗa bisa ƙoƙarinta na kawar da ƴan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya a karamar hukumar.
Ya yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki a kan tsaro a yankin da su tashi tsaye wajen bada gudunmawa wajen samun dawwamammen tsaro a ƙaramar hukumar.
A tsarin rabon tallafin, iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a wajen yaƙi da ta’addanci, za a bai wa kowanne Naira miliyan ɗaya, sai kuma mutanen gari suma kowane za a ba iyalansa dubu ɗari biyar .
Sauran sun haɗa da iyalan waɗanda suka jikkata da na waɗanda suka kuɓuta daga hannun ƴan bindiga da kuma waɗanda suka rasa dukiyoyinsu.