Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar Katsina, Dakta Salisu Bala zango ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai.
Ya ce, gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Dikko Raɗɗa tuni ta yi matsaya na ba za ta bi ƴan bindiga domin sasantawa ba sai dai in su suka nemi buƙatar haka.
Matsayar ta biyo bayan wani labari da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo inda ke nuna cewa jami’an tsaro da jami’an gwamnati da wasu shugabannin ƴan bindiga sun yi zaman sasantawa a garin Batsari.
Kwamishinan ya bayyana cewa duk da ba shi da cikakken bayani kan zaman sansancin da akayi, “matsayin Gwamnatin Katsina na nan ba ta canza ba na ƙin sasantawa da su ƴan bindiga.”
Saidai, ya ce ƙofar gwamnati a buɗe ta ke wajen karɓar ɗan ta’addar da ke bukatar ajiye makaminsa tare da rungumar zaman lafiya.
Labari da ke yawo a yanar gizo har da hotuna ɗauke da jami’an tsaro da wasu jami’an ƙaramar hukumar Batsari da Sarkin Ruma Hakimin Batsari na zaman sasanci a tsakanin ƴan ta’addar yankin da mutanen garin Batsari.