Gwamnatin Katsina ta raba wa ƙungiyoyi kayayyakin aikin gayya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sama da buhunan siminti dubu uku da banduran kwanan rufin gidaje saba’in ne Gwamnatin Jihar Katsina ta sayo domin raba wa ƙungiyoyin aikin gayya a ƙananan hukumomi 18 da ke faɗin jihar.

Mai bai wa gwamnan Jihar Katsina shawara a kan ci gaban al’umma da ƙungiyoyin aikin gayya, Alhaji Bishir Abdullahi Dangote ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamar da rabon kayan kashi na farko wanda ya gudana a harabar ma’aikatar da ke kusa da gidan gwamnatin jihar.

Kamar yadda ya bayyana, kashin na farko da aka ƙaddamar za a tallafa wa ƙungiyoyi 30 ne da suka fito daga kashi na farko na ƙananan hukumomin da za su amfana da kayayyakin wajen ayyukan maƙabartu da masallatai da makarantun Islamiyya da kuma ayyukan magudanan ruwa.

Bishir Dangote ya buƙaci ƙungiyoyin da suka amfana da wannan shiri da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin tallafa wa shirin gwamnatin na inganta rayuwar al’ummar jihar.

Hakazalika, ya gode wa ‘yan majalisar jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa shirin domin ganin ya cimma nasarar da ake buƙata.

Taron ya samu halartar dukkanin ‘yan majalisun ƙananan hukumomin da suka amfana da wakillan al’umma da dai sauran masu ruwa da tsaki a fannin ci gaban al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *