Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta samar da kayyayaki na sama da Naira miliyan 40 na gwaji ga ɗaliban hukumar kwalejin koyon jinya da unguwarzoma dake Katsina da Malumfashi.
Mai ba gwamna shawara akan makarantun kiwon lafiya da sauran hukumomin lafiya Hon. Umar Mammada ya ƙaddamar da kayyayakin a Katsina.
Ya bayyana cewa na’urorin da aka samar irinsu ne ake amfani da su a sauran ƙasashen da suka cigaba, sai ga shi Gwamna Dikko Radda ya kawo su a jihar, yin hakan kuwa ba ƙaramin cigaba aka samu ba a ɓangaren lafiya.
Hon. Mammada ya yi kira ga wanda suka amfana da kayyayaki da su kula sosai wajen ganin an yi amfani da su wajen koya wa ɗalibai aiki da su yadda ya dace.
Ya gode wa gwamnan jihar akan namijin ƙoƙarin da yake yi wajen gyara fannin kiwon lafiya a jihar.