Gwamnatin Katsina za ta ɗauki malaman S-Power 7,000 aiki

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana shirinta na ɗaukar ƙarin malaman makaranta 7,000 a faɗin jihar.

Mai magana da yawun Gwamnan Dikko Umar Raɗɗa, Malam Ibrahim Kaula ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Ya ce, mataimakin gwamnan jihar, Hon. Faruq Lawal Jove ya sanar da hakan a lokacin da yake ƙaddamar da mambobin kwamitin da za su tantance waɗanda za a ɗauka ɗin a ofishinsa.

Mataimakin gwamnan ya ce za a ɗauki malaman makaranta 5,000 dake da shaidar malanta ta ƙasa NCE/Diploma da za su koyar a makarantun firamare da kuma 2,000 masu digiri da za su koyar a makarantun sakandare na jihar.

Kazalika, Mataimakin Gwamnan ya ce kwamitin zai yi bita kan batun malaman makaranta 3,889 da aka ɗauka ƙarƙashin hukumar kula da ilmin firamare ta SUBEB, inda ya ce za a sake tantance su tare da jarrabawa domin tabbatar da ba a yi kitso da ƙwarƙwata ba.

Hon Faruq Lawal Jove ya yi bayani gamsasshe game da yadda shirin ɗaukar aikin zai kasance.

Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Arch Ahmad Musa Ɗangiwa, ya gabatar da mambobin kwamitin da kuma kamfanin da zai shirya jarrabawa ga waɗanda za a ɗauka aikin.

Arch Ahmad Musa Ɗangiwa ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki tsakani da Allah ba tare da nuna son rai ba.

Kwamitin dai na da Dakta Sabi’u Ɗahiru a matsayin shugaba, sai Malam Lurwanu Haruna Gona a matsayin Sakatare.

Sauran mambobin kwamitin su ne, Malam Shamsudden Sani, Dakta Isah Idris Zakari; Mannir Ayuba Sullubawa, Shehu Abdullahi Mohammed da Zakariya’u Musa Doka.

Kwamitin na da wata ɗaya ya gabatar da rahotonsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *