Gwamnatin Katsina za ta biya ƴan fansho duka bashin da suke bi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina za ta biya ƴan fansho duka kuɗaɗen da suke bi nan ba da jimawa ba.

Kwamishinan Kasafin kuɗi, Hussaini Bello ya faɗi hakan a lokacin da ya ke wa manema labarai bayanin kasafin kuɗi na 2025.

Ya ce gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 15 domin biyan ƴan fanshon kuɗaɗensu.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ƴan fansho daga ƙananan hukumomi 34 na jihar za a biya su ne a tsakiyar shekara mai zuwa.

Ya kuma ce cikin kasafin kuɗi na 2025, gwamnatin za ta kashe Naira biliyan 524 daidai da kashi 17, wanda hakan ya nuna yadda gwamnatin Dikko Raɗɗa ta bai wa ayyukan bunƙasa ƙasa muhimmanci.

Haka kuma kwamishinan ya ce gwamnatin ta ware wasu kuɗaɗe da ta saka a kasafin kuɗin domin biyan sabon tsarin albashi na Naira 70,000.

Tuni Gwamna Dikko Raɗɗa ya gabatar da kasafin kuɗi na 2025 ga zauren Majalisar dokoki na jihar.

Ya gabatar da Naira biliyan 682 a matsayin kasafin kuɗin inda bangaren ilimi ya samu kaso mai tsoka na kashi 14.