Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya za su farfaɗo da noman rani a madatsar ruwa ta Sabke da ke ƙaramar hukumar Mai’adua.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a yayin da yake zagayawa da wakilin gwamnatin tarayya kuma bubban darakta na kasafin kuɗi Dr Tanimu Yakubu kurfi domin gane ma idanun su halin da madatsar ruwan ke ciki.
Ya ce zaɓen madatsun ruwa na Sabke, Jibiya da zobe ƙarƙashin shirin sabunta samar da kuɗaɗen bunƙasa ƙasa abin a yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne.
Raɗɗa ya bayyana shirin a wani yunkuri na shugaban ƙasa na ganin duk wani ɗan Najeriya ya sami abinda zai ci akan farashi mai rangwame.
“Arewacin Najeriya na da isasshen fili da wadataccan ruwa wanda ya wuce abinda ake buƙata na noma domin haka wannan shiri zai bawa matasan mu dama su sami abin yi da kuma rage matsalar tsaro da ake fama da shi”inji Dikko Raɗɗa.
Ya ce madatsar ruwa ta Sabke za ta zama wuri da za a iya noman rani na zamani ba tare da dogaro da lokacin damina.
A nasa jawabin shugaban tawagar gwamnatin tarayya Dr Kurfi ya ce wannan shiri na ɗaya daga cikin tsare tsare na gwamnatin tarayya na magance matsalar abinci.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da na Jihar Katsina za su haɗa kan manoman shinkafa da alkama da sauran noman rani a yankin domin ganin sunyi amfani da madatsar ruwa domin samar da abinci a ƙasa.
Dr Kurfi ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatim tarayya za ta duba ta ga nawa ne za ta kashe kafin a fara amfani da madatsar ruwan.