Gwamnatin Katsina za ta gyara cibiyar sarrafa gyaɗa a Kankiya 

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada umurnin da a gaggauta gyara cibiyar sarrafa gyaɗa ta Kankia da aka yi watsi da su. 

Gyaran ya haɗa da gina ƙarin wuraren sarrafa gyaɗar da sayen injinan sarrafawa na zamani, da kuma gyara sauran kayayyakin da suka lalace sakamakon shekaru da dama da rufe cibiyar. 

Wannan yunƙuri na nufin farfaɗo da tattalin arzikin jihar da samar da aikin yi ga ɗinbin matasa. 

Al’ummar jihar nada gwiwar wannan yunƙuri na gwamnati zai zuba jawo hannun jari a ciki da wajen jihar, zai kuma saka jihar Katsina a sahun kan gaba wajen masu noman gyaɗa a ƙasar shekara fiye da hamsin da suka wuce a kasan jihar Kano a matsayin na ɗaya wajen noman gyaɗa da akan santa da ɗaukan gyaɗa amma yanzu ba noman ba dalar.