Gwamnatin Kebbi da kamfanin MSM sun rattaɓa hannu don kafa kamfanin siminti a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Sanya hannu kwanan nan kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tsakanin gwamnatin jihar Kebbi da kamfanin MSM Cement Ltd don kafa wata masana’antar siminti a Maiyama ya zama muhimmin mataki a ƙoƙarin tattalin arziki da masana’antu da gwamnan jihar ya alƙawarta a lokacin yaƙin neman zaɓensa kafin zaɓen 2023.

Kwanaki kaɗan da suka gabata, an kammala wannan yarjejeniya a Gidan Gwamnatin Kebbi da ke Abuja, tare da halartar Gwamna Idris, Shugaban MSM, Alhaji Mu’azzam Mairawani, da wasu manyan jami’an tarayya. Wannan jarin yana ɗaya daga cikin manyan hannun jari da aka taɓa zubawa a Kebbi tun kafuwar ta a 1991, kuma yana zama kyakkyawan misali na nasarar cimma manyan yarjejeniyoyin kasuwanci a ƙarƙashin kowace gwamnati a yankin nan a tarihin baya-bayan nan. Wannan ci gaban yana nuna ƙwarewar jagoranci na musamman da Gwamnan Kebbi mai ci ke da shi.

Yarjejeniyar na da nufin samar da ayyukan yi 20,000 kai tsaye da wasu 25,000 a hanyoyin da ba kai tsaye ba, wanda hakan ke sanya wannan shiri a sahun manyan masu samar da ayyukan yi a wannan yankin na Nijeriya.

Abu mai ƙayatarwa shi ne, ana sa ran masana’antar MSM Kebbi Cement za ta samar da ton miliyan uku na siminti a kowace shekara, tana amfani da sabuwar fasaha da za ta ba da ingantaccen siminti daga cikin mafi kyau a ƙasar nan.

Wannan cigaban ba kawai kafa masana’anta ba ne; yana nuna farkon wani sabon zamani na bunƙasar tattalin arziki da nasarorin masana’antu da za su inganta rayuwar al’ummar jihar Kebbi. Bugu da kari, jarin MSM shi ne kawai matakin farko, wanda ke bude kofar shigowar masu zuba jari na duniya da ke son cin gajiyar dimbin albarkatun ma’adinan da Allah ya hore wa jihar.

A lokacin sanya hannu kan MOU a Abuja, Shugaban MSM ya jaddada cewa daya daga cikin dalilan da suka ja hankalinsu zuwa Kebbi shi ne wadatar ma’adanai masu inganci a yankin, tare da zaman lafiya, yanayi mai kyau ga kasuwanci, da wadatar ma’aikata.

Wajibi ne a fahimci cewa wannan shiri zai zama abin koyi ga sauran masu zuba jari da ke neman cin moriyar damammakin da Kebbi ke da su a fannin hakar ma’adanai.

Misali, wata kamfanin kasar Sin na cikin tattaunawa da gwamnati don binciken albarkatun lithium, wanda zai iya haifar da sama da ayyuka 50,000. Samuwar lithium mai inganci a yankunan Shanga da Fakai yana jan hankalin masu zuba jari daga kasashen duniya.

Lithium, wanda ke da launin azurfa mai haske kuma yana da laushi, shine karfe mafi sauki da aka sani kuma yana daga cikin ma’adanai masu nauyi kadan. Ana amfani da shi a fannoni daban-daban kamar batir, kayan tukwane, gilashi, da magunguna. Misali, lithium yana da matukar muhimmanci wajen samar da batirin lithium-ion da ake amfani da su a motocin lantarki da na’urorin sadarwa. A fannin lafiya kuma, ana amfani da shi a cikin pacemakers da kuma wajen kula da matsalolin hankali irin su hauka da damuwa.

Wadannan ci gaban a Kebbi suna nuna cewa jihar na kara zama cibiyar bincike da hakar ma’adanai masu daraja tare da samun bunkasar tattalin arziki mai kyau. Duk wadannan abubuwan alheri sun samo asali ne daga wani muhimmin abu da aka dade ana bukata a Kebbi: Gwamna mai hangen nesa, wanda ke da basirar jagoranci da tsare-tsaren da za su kawo ci gaba ga al’ummar da Allah ya hore wa arzikin ma’adanai.