Gwamnatin Kebbi ta bai wa ɗan gidan Giro muƙami a hukumar Alhazai

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamna Malam Nasir Idris ya maye kujerar Marigayi Sheikh Abubakar Abddullahi Giro Argungu da ɗansa Malam Hussaini Abubakar Giro a hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kebbi, inda Sheikh Abubakar Giro kafin rasuwarsa mamba ne a hukumar.

Wannan ya biyo bayan wani koke da ƙungiyar Izala ta ƙasa ƙarƙashin jagoranacin Sheikh Bala Lau ta miƙa wa Gwamna Idris ne yayin da suka je ta’aziyya a fadar gwamnatin jihar Kebbi inda suka nemi gwamnati da ta janyo ɗaya daga cikin ‘ya’yan Marigayi Giro a jiki saboda cigaba daga inda ya tsaya.

Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga duniyar Musulmi saboda kasancewarsa mutum mai haƙuri da juriya da sadaukarwa wanda ya fi fifita matsalar al’umma a kan tasa.

Ya qara da cewa duniyar Musulmi za ta daɗe tana jimamin rasuwarsa bisa ga irin gudummawar da ya ke bayarwa wajen da’awa.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙansa ya yi masa sakayya da gidan Aljanna ya bai wa iyalansa da ‘yan uwa da abokansa haƙuri.

Iyalan gidan Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu na miƙa saƙon godiyar su.

A ɗaya ɓangaren kuma iyalan Marigayi Sheikh Abubakar Giro Malam Hussaini Abubakar Giro yana godiya ga ƙungiyar Izala a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau da kuma sauran shuwagabannin ƙungiyoyin addinin Musulunci da sauran al’umma Musulmi da suka halarci jana’izar marigayin daga gida waje musamman Ghana, Kamaru, Nijar da kuma Benin da sauran ƙasashe.

“Haka zalika godiya ga Shugaban Ƙasar Nijeriya da mataimakinsa da kuma gwamnatin jihar Kebbi da Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera da ‘yan majalisarsa da manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da da fatar Allah ya sakawa kowa da alheri.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *