Gwamnatin Kebbi za ta biya kuɗin WAEC kaɗai, inji Magawata

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa wannan shekarar za ta biya kuɗin WAEC kawai ba za ta biya kuɗin NECO ba.

Kwamishinan Ilmi na jihar Alhaji Muhammadu Magawata Aliero ne ya bayyana wa wakilinmu haka a wata zantawa da suka yi ranar Talatar da ta gabata.

Muhammadu Magawata Aliero ya bayyana cewa wannan ya biyo bayan wani zama da ma’aikatar ilimi da masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi a jihar da suka haɗa da ƙungiyar iyaye da malamai (PTA) da ƙungiyar cigaban Jihar Kebbi (Kebbi Development Forum) da kuma SBMC a farko satin nan.

Magawata Aliero ya ƙara da cewa ya kamata a bai wa Kebbi lambar yabo saboda makwabtan jihohin Kebbi irin Sakkwato da Zamfara yau shekaru uku da suka daina biyan kuɗin WAEC, amma Kebbi tana biya yanzu ne ta ga ya kamata iyaye su biya kuɗin NECO ita kuma gwamnati ta biya na WAEC.

Alhaji Garba Manuga Birnin Tudu ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar iyaye da malamai, ya bayyana cewa duk da ya ke ba su zauna da sauran shugabannin ƙungiyar iyaye da malai ba suka bayyana musu ƙudurin gwamnati na janye biyan waɗannan kuɗaɗen wannan shirin bai yi musu daɗi ba saboda ba kowane uba ke iya ɗaukar nauyin biyan waɗannan kuɗin ba. Saboda haka ya kamata gwamnati ta canza shawara, inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *