Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Ƙidaya ta Nijeriya (NPC) ta ce gwamnati za ta ɗauki ‘yan ƙasar miliyan ɗaya aiki domin gudanar da ƙidayar jama’a a shekarar 2023.
Hukumar ta ba da tabbacin cewa, an samar da kyakkyawan tsarin gudanar da ƙidayar don hana ‘yan siyasa da masu mummunar aniya amfani da wannan dama.
Jaridar Daily Trust ta rawaito kwamishinan hukumar mai kula da jihar Ekiti Mista Deji Ajayi na bayyana hakan ranar Litinin a Ado Ekiti a wani taron manema labarai da ya kira kan ƙidayar gwaji da za a gudanar a jihar.
A yayin da yake bayyana muhimmancin ƙidayar jama’a ga gina ƙasa, Ajayi ya ce ƙungiyoyi masu zaman kansu za su yi amfani da ƙididdigar yawan jama’a wajen tsara yadda za a ɗauki matasan Nijeriya aiki ta hanyar sanin adadin yawan jama’a.
“Gwamnati za ta kuma yi amfani da irin wannan ƙididdiga don tsara yadda za a taimaka wa matasanmu, da ɗalibanmu da kuma biyan buƙatun sauran jama’ar ƙasa’ inji shi.