Gwamnatin Tarayya ba za ta amince da ƙarin sama da kaso 60 na farashin kiran waya ba – Minista

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Sadarwa, Bosun Tijani ya nanata cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta bari kamfanonin telekom su ƙara kuɗin kiran waya da kaso 100 ba.

A ƴan shekarun nan ne kamfanonin suka yi ta yunƙurin ƙara farashin sakamakon tsadar kuɗaɗen gudanarwa, hauhawar farashi da rugujewar naira da makamantansu.

Ministan, a wata hira da gidan talabijin na ‘channels’ ya ce gwamnati ta san cewa lokacin ƙara farashin kira ya yi, amma ba za ta amince da ƙarin kaso 100 da kamfanonin suke nema ba.

Ya ce ƙarin a ko’ina bai kamata ya wuce kaso 30 zuwa 60 ba, inda duk abin da ya haura akan haka zai zama cutarwa ga al’umma wanda kuma gwamnati ba za ta so hakan ba.

Ya kuma ce Hukumar Sadarwa ta NCC tana aiki game da batun da kuma ƙoƙarin cimma matsaya a kai.

Ya ƙara da cewa, yana da muhimmanci a duba adadin da kuma tasirin da zai yi wa al’umma da kuma samar da daidaito a ɓangaren.

Kazalika, ministan ya ce akwai buƙatar masu kamfanonin su inganta harkokinsu ga al’umma.