Gwamnatin Tarayya da Nasarawa za su yi aiki tare wajen kare yankunan haƙo ma’adinai

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Nasarawa sun shirya yin aiki tare domin kare yankuna masu arzikin zinari a jihar Nasarawa da kuma kare iyakokin Abuja da Nasarawa.

Ministan Bunƙasa Ma’adinai, Architect Olamilekan Adegbite, shi ne ya bayyana hakan sa’ilin da ya karɓi baƙuncin Gwamna Abdullahi Sule a ofishinsa da ke Abuja a Talatar da ta gabata.

A cewar Ministan Gwamnatin Tarayya ta kashe maƙudan kuɗaɗe har biliyan N15 kan harkokin ma’adinai a sassan ƙasa ƙarƙashin shirinta na aikin binciko inda arzikin zinari yake a Nijeriya inda ta gano hakan tsakanin Jihar Nasarawa da Abuja.

Ya ce tuni gwamnati ta soma tallata bayanan da ta tattara a mataƙin ƙasa da ƙasa domin aikin haƙo zinarin, tare da cewa ‘yan kasuwa da dama sun nuna ra’ayoyinsu kan aikin inda za su shigo su yi aiki daidai da dokar ƙasa.

Sai dai ministan ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun wasu na aikin haƙar zinari ba a bisa ƙa’ida ba tare da bada misalin abin da ke faruwa a jihar Zamfara wanda har ya kai ga gwamnatin jihar ta kafa dokar haramta harkokin haƙar zinari.

Adegbite ya ce Gwamnatin Tarayya na yin dukkan mai yiwuwa wajen hana haramtattun ayyukan ginan zinari da batun kan iyaka a yankunan Nasarawa da Abuja.

A nasa ɓangaren, Gwamna Engineer Abdullahi Sule, ya yi godiya ga ministan da ma Gwamnatin Tarayya dangane da ayyukan binciken inda ake da zinari a faɗin ƙasa da kuma bayanan da suka tattara. Yana mai cewa a shirye jiharsa take ta bada dukkanin goyon bayan da ake buƙata.