Gwamnatin Tarayya na shirin cire dokokin kariyar Korona

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cire dokar da ta wajabta amfani da takunkumin baki a wajen mu’amalar jama’a da wuraren taruka da ofisoshi, don hana yaɗuwar annobar Korona.

Kwamitin Shugaban Ƙasa na Covid-19 wanda Sakaten Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ke jagoranta, shi ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa saka takunkumin a wuraren taron jama’a zai kasance zaɓi ga wanda ke buƙata, sai dai kuma dokar za ta fara ne bayan hutun Easter.

Yawancin ƙasashe a duniya da dama sun sassauta yawancin dokar kariya da annobar Korona bayan karɓar allurar rigakafin cutar.

Kwanan nan Daular Saudiyya ta cire dukkan dokokin da ta sanya na kariya da annobar don bai wa mahajjatan duniya damar sauke farali yayin aikin Hajjin 2022 a Makka. Sai dai dole ne mahajjata kafin su shiga ƙasar sai sun tabbatar da sun karɓi allurar rigakafi.

Ƙasar Amrika ma ta janye dokar amfani da takunkumin fuska, sai kuma kwanan nan ita ma ƙasar Ghana ta bayyana amfani da takunkumin ba dole ba ne a yanzu.

Sai dai dokar takunkumin a Nijeriya za ta cigaba da yin aiki a a cikin bankuna, manyan kantina. Amfanin da takunkumin zai zama zaɓi kamar yadda sanarwar ta ce.