Daga AMINA YUSUF ALI
Gwamnatin tarayya ta ba da sanarwar sake waiwayar harajin shigo da kayan waje (IAT) a matsayin wani ɓangare na tsara dokar harajin Gamayyar kasuwanci ta Afirka (ECOWAS) (CET) 2022-2026, wannan ya sa ta yi ƙari a kan haraji ga jasashe masu shigo da shinkafa, alkama, barasa, da sauran hajoji guda 189.
Wannan sabon ƙarin harajin na shekarar 2023, ya ɗaga harajin kan shinkafa da ta haura kilo 5, ko mai yawa amma a rarrabe zuwa kilo 5, to za a biya harajin kaso 60, wanda kaso 50 ake biya a baya.
Hakazalika, shigo da alkama ko fulawar cin-cin za a biya kaso 70, wanda ake biyan shi ma kaso 50 a baya.
Ministar kuɗi da kasafi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana a cikin wani jawabi cewa, wannan shi ne son ba da tabbacin cewa, shugaban ƙasa da tabbatar da sabuwar dokar ECOWAS ta 2023 ta ƙarin haraji a kan kayan da aka shigo da su daga waje, zuwa cikin Afirka.
Kuma a cewar ta, an yi ƙarin harajin ne a kan shinkafa, alkama, taba sigari, barasa da sauransu.
Haka nan, Ministar ta ƙara da cewa, wannan sabuwar dokar ƙarin harajin ta haɗa har da ƙasashen da suke da shigo da kaya a karon farko zuwa ƙasashen Afirka.
Wannan sabon harajin zai ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen Afirka mambobin ECOWAS kuma ta ƙarausu ƙarfin kasuwanci.
Sannan ana sa ran dokar harajin ta fara aiki tun ranar 1 ga watan Mayun shekarar bana ta 2023.